Rundunar ‘yan sandan Nigeria ta bada rahoton afkuwar hatsarin da ‘yan fashi suka janyo inda mutane akalla goma sha uku suka rasa rayukansu.
Hatsarin ya afku ne bayan da ‘yan fashi suka tsaida motar fasinja suka tilastawa fasinja fitowa daga motar da tilasta masu kwanciya a kasa. Yayin da suke kwance kasa ne kuma sai wata mutar ta bullo a guje tabi ta kan fasinjan.
’Yan sanda suka ce ‘yan fashin sun tsaida motar fasinjan ne a kan hanyarta ta zuwa birnin Abuja Talatar da ta gabata.
A wani labarin kuma, kamfanin Mai na Shell a Nigeria ya bada sanarwar daukan nauyin gurbacewa da bulbular mai da suka afku a wasu manyan rijiyoyin mai biyu dake Nigeria a shekarar 2008, gurbacewar da ta janyo asasar rafukan da masunta kusan dubu saba’in ke kamun kifi.
Lauyoyin dake wakiltar al’ummar yankin Bodo dake ogoniland, sun shigar da kara a kutun Ingila suna neman kamfanin man na Shell ya biya su diyya, diyyar da ka iya kaiwa miliyoyin Daloli domin inganta halin zaman rayuwarsu.
Masana sun yi hassashen cewa za’a bukaci kudi sama da Dola miliyan dari domin gyara rafukan bakin tekun domin inganta muhallin yankin da halin zaman al’umma. Kamfanin Mai na Shell bai bayyana komai ba kan karar da al’ummar Ogonin suka shigar a kotun Ingila ba.