Bishop Stephen Dami Mamza na darikar Katolika ya shaidawa muryar Amurka ya ce, suna kwaikwayon ayyukan agaji da Mama Teresa ta kasar Indiya da Paparoma ya aiyana waliyiya makon jiya saboda ayyukan agaji da ta aiwatar kafin rasuwarta a shekara ta 1997.
Ya ce rabon tallafin gida-gida ya biyo bayan la’akari da majami’ar ta yi na mafi yawan lokuta tallafin da kungiyoyi ke bayarwa baya isa ga rukunin ‘yan gudun hijira da suka sami mafaka a gidajen ‘yan uwa da dangi.
Wasu daga cikin matan da suka anfana daga tallafin sun fada cikin hirar su da wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu, sun nuna farin cikinsu da kungiyar ta bi su da tallafin har gida kamar yadda zaku ji malama Hauwa Isa da Tani John ke fadi cikin wannan rahoton cewa shine karon farko da irin wannan tallafi ya shiga hanunsu.
Saurari rahotan Sanusi Adamu.