Malam Yushau Aliyu yace rufe iyaka da hana shigo da abinci ya kara kawo ta'azzara lamura.
Yace ana noma kuma saboda noman da mutane su keyi ya sa farashin tumatur ya koma nera dari ukku kowane kwando saboda tsananin noma. Amma yanayin hana samun dalar Amurka ya haddasa tsadar abinci.
Yushau Aliyu yace duk abubuwan da kasar ke ci ko sha ko sanyawa a jika kashi saba'in cikinsu daga kasashen waje ake shigo dasu. Har magani daga waje ake shigo dashi.
Talauci ya fi kamari a arewacin kasar kuma kayan da ake shigowa dasu ta kan iyakokin kasar su ne suke taimakawa talaka na samun abun da yake sayarwa. Rufe iyakokin ya kara jefa talakawan arewa cikin wani bala'in mawuyacin hali.
Kafin gwamnati ta hana wani abu dole sai ta samar da yanayin da zai taimakawa talakawa.
Wani dan jam'iyyar APC Garba Tela yace akwai bukatar sauya manufofin tattalin arziki na gwamnatin Buhari. Yace a irin tafiyar da ake yi yanzu, shin ana son a rusasu ne ko me nene ake nufi.
To saidai shahararren malamin addinin Islama Shaikh Yakubu Musa Katsina yace gaggawa ba zata haifar da alheri ba. Yace ya kamata jama'a su gane cewa kuncin da ake ciki yanzu sakamakon mummunan shugabancin da aka samu ne da. Abu na biye dashi ita ce matsalar Boko Haram da ta hana kasuwanci da noma.
Ga rahoton Lamido Abubakar da karin bayani.