Wakilin Muryar Amurka a birnin Maiduguri y ace ga dukkan alamu jita-jitar da aka yi ta yadawa cewa ‘yan Kungiyar Boko Haram na gab da shigowa cikin birnin Maiduguri ba gaskiya ba ne. Y ace amma jita-jitar ba za ta rasa nasaba da hare-haren da kungiyar ke kai wa a garuruwan kewaye ba.
Wakilin namu, Haruna Dauda Biu ya gaya ma Halima DJimrao ta wayar tarho cewa gaskiya ne sojojin Nijeriya sun yi nasara kan ‘yan Boko Haram a samamen baya-bayan nan da su ka kai kan kungiyar a yankin Konduga. Ya ce an ma yi ta samun Karin gawarwakin ‘yan kungiyar a daji. Saboda haka, in ji shi, a yanzu adadin ‘yan kungiyar da aka kashe a yankin na Konduga zai haura 100.
Haruna y ace ya ma ga wani dan Boko Haram din da ya gudo ya shigo cikin birnin Maiduguri saboda tsananin zafin yakin da aka tafka a yankin na Konduga. Ya ce su wajen 10 ne su ka shigo birnin na Maiduguri saboda tsananin yakin da aka yi a dajin na Konduga. Haruna ya ce ya ga ‘yan Kato Da Gora na ta masa tambayoyi shi kuma ya na amsawa, ya na ba su hadin kai.