La’akari da wasu tarin bukatu da ke tattare da tsarin gudanar da ma’aikatun gwamnati ya sa majalisar dokokin Nijar amincewa kudirin dokar shekarun shiga ritayar ma’aikata a jerin sauye-sauyen da hukumomi suka bullo da su don inganta rayuwar ma’aikata da iyalansu.
Matakin na nufin daga yanzu an kara wa ma’aikata shekaru 2 don ci gaba da aiki kafin su shiga ritaya, ma'ana yanzu shekarun ritaya sun tashi daga 60 zuwa 62.
Shugaban kwamitin kula da sha’anin doka a majalisar dokokin kasa Hon. Kalla Moutari ya yi karin haske, ya na mai cewa kudirin ya na ba da dama ga tsofaffin ma'aikata su yi renon sabbi. Bayan haka kudirin zai kara wa ma'ikata alawus.
Kungiyoyin kwadago sun yaba da wannan mataki da su ka ce sun jima suna fatan ganin an tabbatar da shi don jin dadin rayuwar ma’aikata, kamar yadda mataimakin sakataren hadaddiyar kungiyar kwadago ta CDTN Ibro Kane ya bayyana.
Kungiyoyin matasa a na su bangaren sun yi watsi da kudirin gwamnatin ta Nijer, kasar da alkaluman kididdiga suka tabbatar cewa mafi yawan al’ummarta matasa ne.
A tunanin rukunin na matasa karin shekarun ritaya abu ne da zai jefa dimbin yaran da suka kammala karatu cikin halin zaman kashe wando.
To sai dai majalisar dokokin ta ce ba ta manta da bukatun matasa ba kafin ta yi na’am da wannan doka.
Dukkan ‘yan majalisa 94 da suka halarci zaman mahawarar ne suka yi na’am da sabuwar dokar fasalta tsarin aikin gwamnatin ta Nijar, wacce aka ayyana cewa za ta soma aiki daga ranar 1 ga watan nan Mayun 2023.
Saurari rahoton cikin sauti: