Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Bukaci Buhari Ya Ayyana Dokar Ta Baci Akan Sha'anin Tsaro


Majalisar Wakilan Najeriya.
Majalisar Wakilan Najeriya.

Yanayin tabarbarewar tsaro a dukkan sassan Najeriya ya sa majalisar wakilan kasar ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta baci akan sha’anin tsaro a kasar.

Daga cikin matsayar da aka cimma a zaman zauren majalisar wakilan na ranar jiya Talata, majalisar ta yi kiran da a dauki karin ma’aikata da jami’ai a hukumomin tsaron kasar, ta yadda za su sami isassun ma’aikata da zai ba su damar shawo kan kalubalen tsaro.

‘Yan majalisar sun kuma ce za su gayyaci mai baiwa shugaban kasa shawara a sha’anin tsaro, da manyan hafsoshin tsaro, da ma dukkan shugabannin hukumomin tsaro na kayan sarki, domin su yi bayani akan halin da kasa take ciki akan sha’anin tsaro.

Haka kuma majalisar ta umarci dukkan kwamitocin ta na sha’anin tsaro, da su gaggauta soma cikakken bincike akan dukkan kayan aiki da makamai na rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, su kuma gabatar da rahoton binciken na su a cikin makwanni 4.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila

Majalisar ta kuma yi kira ga bangaren shari’a da ya gaggauta yanke hukunci ga wadanda ake tuhuma da laifukan ta da kayar baya, ta’addanci da sauran manyan laufuka, wadanda ke zaman jiran hukunci.

Karin bayani akan: Sani Bello, Biafra, Majalisar Wakilai​, Boko Haram​, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Bugu da kari, majalisar wakilan ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kan su, ta yadda za su sami damar biyan bukatun jama’arsu a yankunan karkara.

Majalisar dokokin ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa hukumomi da jami’an tsaro a fadin kasar, inda kuma ta jajantawa iyalai da ‘yan uwan dukkan wadanda matsalar tsaro ta rutsa da su, kana kuma ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tallafa musu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da zaman dar-dar tare da fargaba, sanadiyyar kara yawaitar kalubalen tsaro a fadin kasar.

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnan jihar Naija Sani Bello, ya yi koken cewa kungiyar Boko Haram ta kafa tutocinta a wasu sassan jihar, yayin da al’ummar garuruwa fiye da 50 sun yi kaura daga gidajensu.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Rahotanni sun bayyana adadin wadanda suka mutu daga cikin daliban jami’ar Greenfield ta Kaduna da aka sace ya karu zuwa 5 bayan da ‘yan bindigar da suka sace su suka dada kashe wasu 2.

A wannan ranar ne kuma wasu mahara da ake zargin ‘yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra suka kai farmaki a Awkuzu da ke karamar hukumar mulki ta Oyi a jihar Anambra, inda suka kashe mutane akalla 12.

'Yan Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra, IPOB
'Yan Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra, IPOB

A jihar Rivers ma ‘yan bindiga sun kai hari suka kashe kimanin sojoji 6 a yankin Omelema da ke karamar hukumar mulkin Abua/Odual.

Haka kuma wasu ‘yan bindiga sun kai hari a jami’ar koyon aikin gona ta tarayya a Makurdi ta jihar Benue inda suka yi awon gaba da dalibai 3.

A jiya ne dai shugaba Muhammadu Buhari, ya nemi kasar Amurka da ta kawo wa Najeriya dauki, duba da yadda matsalar tsaro ke kokarin kassara kasar.

A can baya dai majalisar Wakilai ta yi yunkurin gayyatar shugaba Buhari domin bayyana a zauren majalisar ya kuma yi bayanin yadda ake ciki a sha'anin yaki da matsalar tsaro.

Da farko ya amince zai amsa gayyatar majalisar, amma daga baya ya sauya shawarar cewa ba zai bayyana a gaban majalisar ba a wannan lokacin, saboda wasu dalilai na siyasa.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG