Bincike ya nuna cewa ana safarar fatar jaki zuwa kasashen waje, kuma yin haka ya fara rage yawan jakuna musamman a Najeriya.
Majalisar wakilan Najeriya ta ce abinda ya fi daukar hankalin ta shi ne, idan aka bari jinsin jakuna ya kare a duniya to mutanen karkara musamman a jihohin arewacin Najeriya za su wahala sosai, domin jaki dabba ce da suke amfani da ita wajen sarrafa kayayyakin gonakinsu. Haka kuma wuraren da ake fama da karancin ruwa, da jakuna ake amfani wajen jan ruwa, da daukar sa, a wasu kauyukan ma, da jaki ake kai amarya.
Honorable Garba Datti, shi ne yayi yunkurin kudurin dokar, ya bada dalilin cewa a Najeriya mutane da dama sun dogara ga jaki wajen neman abinci, kuma a yanzu haka safarar sa da ake yi zuwa kasashen waje shi ya sa ya yi tsada sosai, daga Naira dubu 15 yanzu ya kai Naira dubu 90, saboda haka sannu a hankali talaka zai wahala wajen samun jaki.
Garba Datti ya kuma ce kasar Pakistan ita ce ta fara yin irin wannan dokar sannan kasashe irin su Nijar da Habasha suka bi sawu.
Amma ga Haruna Ibrahim, jam'i a Cibiyar Binciken Dabbobi da Albarkatun Gona a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, yana ganin gara a hada hannu da manyan 'yan kasuwa a samo hanyar yawaita jakuna a duniya maimakon hana safarar su.
Shi kuwa Simon Pope, na kungiyar Donkey Sanctuary Skins Campaign da ke kasar Ingila ya ce su na goyon bayan dokar ta hanyar bi a hankali domin yin fadakarwa akan amfanin jakuna ga rayuwar al'umma, saboda haka yana ganin hana safarar su shi ne mafi a'ala.
Ga karin bayani cikin sauti daga Medina Dauda.
Facebook Forum