Saura kwana daya kamin Amurka ta kure wa’adi kan bashi da ake binta, majalisar wakilan kasar ta amince da kuduri da aka cimma yarjejeniya da zai kauda kasa biyan nauyi dake kan Amurkan.
A kuri’a da suka kada a daren jiya litinin, wakilan majalisa 269 ne suka amince da kudurin, yayin da 161 suka ki amincewa.
Dokar zata baiwa Amurka ikon ci gaba da karbar bashi domin tafiyar da ayyukanta, kuma dokar zata zabtare kudade da gwamnati take kashewa dala milyan zambar daya a cikinn shekaru gomamasu zuwa.
Baki daya dai dokar bata sami farinjinin da ake bukata ba. Domin a gefe daya, ‘yan rikau sun ce dokar bata rage yawan kudin da Gwamnati ke kashewa ba sosai, su kuma masu sassaucin ra’ayi suka ce kudin da aka yanke yayi yawa, kuma gashi dokar bata kara haraji kan masu hannu da shuni ba.
Duk da haka galibin wakilai suka ce gara haka, maimakon ace Amurka ta gaza biyan bashin dake kanta. A cikin yinin yau ne ake sa ran majalisar dattijai zata kada kuri’a kan kudurin, kuma duka shugabannin jam’iyun biyu sun ce yarjejeniyar zata sami amincewa. Daga nan zasu aike da kudurin zuwa ga shugaba Barack Obama domin ya rattaba hannu.