Shugaba Barack Obama yace an samu nasarar cimma daidaituwa tsakaninsa da shugabanin Majaisun kasar, domin kara yawan kudin da Amirka ka iya karba ranche, kuma gwamnati ba zata yi jinkirin biyan bashin dake kanta ba.
A jiya lahadi da dare shugaba Obama ya bada sanarwar shawarar wannan yarjejeniya a fadar shugaba ta White House Yace shirin ya tanadi rage kudin da gwamnati ke kashewa da dala triliyan daya cikin shekaru goma masu zuwa, kuma an kafa wani kwamiti a Majalisar dokoki da zai yi nazarin kara rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa.
Shugaba Obama ya baiyana yarjejeniya a zaman ta yi da wajewa, da ta baiwa kasar damar kaucewa kasa ko kuma jinkirin biyan bashin dake kanta.
Litinin ake sa ran Majalisar wakilai data dattijai zasu jefa kuri'a akan yarjejeniyar. Amincewa ta karshe zata kara yawan kudin da Amirka ka iya karba bashi kuma ta ci gaba da biyan bashin da ake binta.
A duk tsawon jiya lahadi, kasuwanin hanayen jari anan Amirka da sauran kasashen duniya suke ta nazarin abubuwan da suka faru a birnin Washington DC. Idan har zuwa talata ba'a cimma yarjejeniya, ko yi da wajewa ba, to zai zama koma baya ga tattalin arzikin duniya da ke kokarin farfadowa daga rikicin kudi da duniya ta fuskanta.
Dukkan bangarorin sun yarda da bukatar dake akwai na rage kudin da Amirka ke kashewa da kuma karan yawan kudin da zata iya karba ranche. Dukkan bangarorin dai, sun yi makoni suna kokarin ganin yadda za'a rage kudin da Amirka ke kashewa.