Ko da ya ke wasu ‘yan Najeriya na sukar sha'anin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, majalisar wakilan kasar ta yi ikirarin cewa kasar tana cikin yakin neman tsira saboda tana fama da dumbin matsaloli a daidai lokacin kaddamar da kwamitin wanda zai sake duba kundin tsarin mulki na 1999 kamar yadda aka gyara.
Daya daga cikin 'ya'yan kwamitin mai wakiltar kwaryar Zaria, Abbas Tajuddeen, ya fadi cewa a wannan karni da ake ciki, akwai kyakkyawar fata kwamitin zai duba muhimman sassa inda ake ganin akwai kalubale, kamar fannin ba bangaren shari'a cin gashin kai domin inganta damokradiya.
Shi kuwa Kabiru Alhassan, dan majalisa mai wakiltar Rano Bunkure da Kibiya a jihar Kano, cewa ya yi kowanne abu na da nashi tasirin sai dai babban al’amari da ke sa a kai ruwa rana a duk lokacin da za a yi gyaran kundin tsarin mulki shi ne kiraye-kirayen kara yawan jihohi, domin kowa yana so a ba yankin da ya fito.
Duk da wannan jan aiki da majalisar ta ce za ta yi wajen gyara gibin da ke cikin kundin mulkin, daya daga cikin shugabannin jam’iyyun kasa Falalu Bello, wanda shi ne shugaban jam’iyyar PRP, ya ce duk abin da ake so a yi yanzu an yi shi a baya.
Ya kuma ce yana goyon bayan shugabanin Arewa su sake duban kundin don fito da tsarin da ya fi dacewa da al’umma.
Wannan kwamiti dai na mutun 54 na majalisar wakilai zai hade da mutum 56 na bangaren majalisar dattawa domin gyara kundin kasar.
Facebook Forum