Kusan duk manyan tituna dake cikin birnin Maiduguri cike suke da hotunan masu neman tsayawa takara.
Tuni dai 'yan takara da dama suka nuna sha'awarsu neman mukamai daban daban. Mafi yawansu na kokarin shiga takarar fitar da gwani ne na jam'iyyarsu. Amma wani batu na kokakrin kunno kai a jam'iyyar APC.
Ana zargin cewa gwamnan jihar Kashim Shettima ya saye duk tikitin 'yan takara musamman na 'yan majalisu na jam'iyyarsa, wato APC. An ce shi da kansa zai rabawa 'yan takaran da yake so. Lamarin ya sa wasu magoya bayan wani dan takara sun bara.
Malam Muhammed Bulama daga karamar hukumar Jere yace sun biya kudin sayawa dan takarar da suke so tikiti ranar Juma'a amma da suka je ofishin jam'iyyar babu kowa duk da cewa jiya ce ranar karshe da kowa zai mika takardarsa. Yace su yanzu basu san abun da suke ciki ba.
Alhaji Muhammed Ayuba Bello mai neman tsayawa takarar kujerar dan majalisar wakilai daga hukumar Jeren yace shi ma ya biya kudinsa a banki kamar yadda aka tsara kuma ya je neman tikitin amma har yanzu babu wani bayani. Yace lamarin ya daure masu kai. Yace yanzu suna jiran gwamna ya fada masu wani abu.
Shugaban jam'iyyar APC reshen Borno Alhaji Abubakar Dalori yace korafin 'yan jam'iyyar ba gaskiya ba ne. Za'a baiwa kowa damar shiga zaben. Amma batun sayar da tikitin an daga shi har zuwa wani lokaci.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.