Taron 'yan majalisar ya samu halartar ashirin da daya cikin su ashirin da hudu. Wadanda basu samu zama a taron ba sun bada goyon bayan duk wani kudurin da majalisar ta dauka.
Adamu Dala Dogo shugaban kakakin majalisar shi ya shugabanci taron. Ya bayyanawa wakiliyar Muryar Amurka dalilin zamansu. Yace sun cimma matsaya akan jita-jita da rudu da 'yan jam'iyyar PDP su keyi cikin jihar. Suna yayatawa cewa akwai 'yan majalisar da zasu bar jam'iyyar APC su koma PDP. Har ma suna cewa wasu zasu samu 'yan majalisar domin a tsige gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Geidam. Yau sun tabbatarwa duniya cewa wannan magana ta 'yan adawa ce ta PDP amma su a Yobe basa yin PDP. Babu dan majalisa daya da zai koma PDP. Sun amince da ayyukan gwamnan kuma shi ne zai sake tsayawa dan takarar jam'iyyarsu a zaben 2015.
Kowane dan majalisar yayi magana daya bayan daya. Waccan magana sun koreta domin magana ce ta karya ta PDP da mazauna Abuja masu son su kawo rudu domin su cuci mutanensu su karbi kudi su saka a aljihunsu.
Abun da 'yan majalisar suka yi ra'ayin al'ummominsu ne inji kakakin majalisar. Babu dan majalisa da yayi magana sai da ya tuntubi mazabarsa.
Akan ko zasu yi irin abun da 'yan majalisar Adamawa suka yi sai kakakin majalisar yace ai Adamawa jihar PDP ce kuma an san jam'iyyar da cin amana koma manyan PDP suna cin amanar juna. Wai su 'yan APC na Najeriya gaba daya ba'a sansu da cin amana ba. Ba kuma za'a iya yin anfani da kudi a yaudaresu ba. Basa son kudi kuma basu gaji kudi ba.
Ga rahoton Sa'adatu Fawu.