A cikin jawabin da yayi lokacin tunawa da cikarsa shekaru saba'in da uku da haihuwa a duniya Janaral Babangida ya roki 'yan Najeriya da su yi hakuri akan tashe-tashen hankula dake faruwa musamman a arewa maso gabas. Yace gwamnatin tarayya na iyakacin kokarita shawo kan lamarin amma kuma zai dauki lokaci. Ya kwatanta lamarin da rikicin da ya kai kasar ga yakin basasa na shekara uku.
Alhaji Ibrahim Dogarai Ningi jigo a jam'iyyar APC ya mayar wa Janaral Babangida martani dangane da kalamunsa. Yana tambayar Janaran kalamun nasa nuni ne cewa yana goyon bayan Shugaba Goodluck Jonathan ne domin ya samu ya zarce. Rikicin da Boko Haram keyi yace a gurinsu ba yaki ba ne. Wani abu ne shiryayye domin a kashe al'ummar Najeriya musamman 'yan arewa. Ko gwamnati ta yadda ko ta ki yadda tana da sha'awa a ciki.
Alhaji Ibrahim yace dattawa 'yan arewa idan da gaske su keyi yakamata su gurfanar da gwamnatin Goodluck dashi kansa Goodluck a kotun aikata manyan lafuka ta duniya. An ce kasashen waje sun shigo amma da suka leka suka ga ba gaskiya ciki sun janye. Shi kuma Janaran da yake cewa za'a warware matsalar cikin shekara uku to idan yana tunanen wata murdiya ne a zabe mai zuwa bashi da sauran kwanciyar hankali.
Akan Nuhu Ribadu Alhaji Ibrahim yace yana cikin mutanen dake son yiwa Janaral Buhari zagon kasa. Lokacin da ya zauna EFCC tsohon shugaba Obasanjo yayi anfani dashi. Saboda haka 'yan Najeriya da 'yan Adamawa sun sanshi. Yanzu ta bayyana a kansa. Mutanen Adamawa ba zasu bari maha'inci ya shugabancesu ba.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.