Jam'iyyar PDP tana zargin za'a yi anfani da kudin ne domin siyasa , wato jam'iyyar APC ce zata yi anfani da kudin domin neman zabe.
Alhaji Ibrahim Milgoma shugaban jam'iyyar PDP a Sokoto yace gwamnan da zai ciwo bashin sauransa wata tara ya kare wa'adin milkinsa. Yace kowa ya sani cewa lokacin da ya karbi milki a hannun Alhaji Attahiru Bafarawa ya bar masa nera miliyan dubu goma sha uku a baitalmali. Bai bar masa bashi ba. Amma a halin da ake ciki yanzu bayan basukan dake kan gwamnatinsa yanzu kuma zai kara ciwo bashi ya karawa gwamnatin nauyi. Yace jam'iyyar PDP bata yadda ba kuma duk bankin da ya ba gwamnatin bashi ya san inda zai nemo kudinsa.
Alhaji Ibrahim ya cigaba da cewa kowa ya san gwamnatin tarayya na ba jihar kudi a kan kari. Lokacin tsohon gwamnan jihar Attahiru Bafarawa kudin da gwamnan yanzu ke samu ya ninka nashi sau uku amma kuma yayi ayyuka da suka anfani jama'a. Sabili da haka babu wani dalilin karbo wani bashi.
Da yake mayar da martani kakakin majalisar jihar Lawal Muhammed Zayyana ya bayyana zargin a zaman mara tushe inda yace sun yi hakan ne domin ciyar da jihar gaba. Yace su bankuna suka ce zasu ba gwamnatin bashi domin ta kammala ayyukan da ta fara yi. Gwamna yayi tunane su ma 'yan majalisa sun ga ya dace a karasa ayyukan da aka fara yi cikin wa'adin wannan gwamnatin. Doka ta basu ikon su yi abun da suka yi kuma su ma 'yan PDP dake majalisar sun amince. Duk wanda yake dan Sokoto ya ga ayyuka manya manya da gwamnan ya soma yi domin haka wajibi ne a kammalasu.
Ga rahoton Umar Faruk Sanyinna.