Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yayi kira ga hukumomi a jamhuriyar Demokaradiyar Congo cewa kada su kara jinkirta babban zaben kasar , suyi kokari suyi zaben kamar yanda aka tsara yi a karshen wannan shekara.
A cikin wannan dambarwar siyasa a kasar, akwai yiwuwar fadawa cikin wani rudami da zai sa a sake dage zaben, a cewar Antonio Guterres, a cikin rahoton da ya aikewa kwamitin sulhun a kan ayyukkan hukumar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo da ake kiranta MONUSCO.
Gwamnatin da yan adawa sun kulla wata yarjejeniya a ranar 31 ga watan Disamban 2016, wanda ke kira ga shugaba Joseph Kabila ya sauka daga mulki bayan zabe a 2017. Amma sai aka yi ta jinkirta wannan zaben, lamarin da ya janyo yakin basasa a kasar, kuma ya haifar da fargaban cewa Kabila mai shekaru 46 a duniya zai nemi karin wa’adin mulki don ya dora a kan shekaru 17 da ya kwashe yana mulkin kasar.
Yanzu dai zabukkan da zasu hada da na yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi, an shirya za’a yi su ne a ranar 23 ga watan Disamban wannan shekarar 2018.
Facebook Forum