Babban sakataren MDD yayi kira ga manyan yan siyasar Congo da su bada cikakken hadin kai ga yarjejeniyar da suka kulla ta 31 ga wata Disemban 2016 wanda ya bukaci Kabila ya sauka daga mulki bayan zabe.
Amma kuma ana ta jinkirta zabukan da akayi alkawarin gudanarwa a shekarar 2017 da ta kare, lamarin dake ci gaba da haddasa tashe tashen hankula da kuma haifar da fargabar Kabila na niyar yin tazarce.
Shi dai Kabila mai shekaru arba'in da shida a duniya ya kwashe shekaru goma sha bakwai yana shugabancin kasar Congo-Kinshasha kuma har yanzu yana nan daram akan karagar mulki, duk da cewar wa’adinsa na biyu ya kare tun a cikin watan Disemban shekarar 2016.
Facebook Forum