ABUJA, NIGERIA - Kafa Kwamitin binciken ya biyo bayan wani kudurin zargin badakala ne da Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya kawo zauren Majalisar Dattawan, to saidai wasu Sanatocin na ganin binciken ba zai yi wani tasiri ba.
A cikin jawabinsa ga Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce rahoton da Bankin Raya Kasa ya fitar a ranar 13 ga watan Yuli na wannan shekara da muke ciki, ya bayyana yadda aka kasafta Naira biliyan 483 a matsayin lamuni da ya kamata a tallafa wa kananan masana'antu domin ceto su daga rugujewa.
Ndume ya ce abin da ya daga masa hankali shi ne cewa kashi 11 cikin 100 na Kudin ne aka ware wa jihohi 19 na Arewa, wanda ya kama Naira biliyan 53 da miliyan 130 kacal, amma Jihar Lagos ta samu kashi 47 cikin 100, wanda ya kama Naira biliyan 227 da miliyan 10 ita kadai.
Ndume ya ce an kafa Bankin Raya Kasa wato DBN ne domin ya rage matsalolin kudade da kananan hukumomi da matsakaitan kamfanoni ke fuskanta a kasar ta hanyar samar masu da bashin kudaden ta hanyar da za ta dace da kasuwa mai dorewa domin a samu a farfado da tattalin arzikin kasa cikin gaggawa amma haka bai samu ba, sai balaín talauci da al'umma ke kuka akai.
Amma Sanata mai wakilta Katsina ta Arewa Ahmed Babba Kaita, ya na mai ra'ayin cewa kafa wannan kwamiti na bincike a daidai wannan gaba da mulki ya riga ya zo karshe, bata lokaci ne kawai. Babba Kaita ya ce an riga an bar gini tun rani, domin a yanzu haka zai yi wuya kwamitin ya samu bayanai kai tsaye domin yawancin mutane suna siyasa ne yanzu. Babba Kaita ya ce babu wani amfani da kwamitin zai yi wa kasar a yanzu.
Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa, Mohammaed Sani Musa ne ke jagorantar kwamitin, tare da Sanata Abdullahi Ibrahim Danbaba da Sanata Ayo Akinyelure da Sanata Mathew Urhoghide, sai Sanata Uche Lilian Ekwunife da Sanata Sadiq Umar da kuma Sanata Mohammed Ali Ndume. An ba su makonni biyu su kammala aikin binciken, su gabatar wa Majalisar da rahoto.
Saurari cikakken rahoton daga Medina Dauda: