Amma majalisar dattawan Najeriya ta nuna rashin gamsuwarta da tsarin gwamnatin kasar na daukan matasan aiki.
Shugaban kwamitin labarai na majalisar Sanata Aliyu Sade Abdullahi shi ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da Muryar Amurka a garin Borgu cikin jihar Neja.
Yace ko kadan basu gamsu da yadda aka tsara za'a dauki matasan ba. Yace su 'yan majalisa suka amince a yi aikin. Amma da aka zo aiwatar da aikin sai aka ba wasu can daban. Su kuma sun dauki mutanen da su 'yan majalisa suka ce basu yi kama da wadanda suka sani ba.
Wani abun da ya cuci mutane shi ne kananan hukumomin dake karkara basu da wuta kuma basu da yanar gizo kuma an ce dole a yi anfani da komfuta da yanar gizo. Wannan ba adalci aka yi masu ba.
Majalisa ta kai korafinsu ga wadanda aka ba su aiwatar da aikin.
Wadanda aka zanta dasu sun ce basu samu ba. Wasu sun sha yawo suna neman inda zasu yi anfani da yanar gizo amma hakonsu bai cimma ruwa ba.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.