Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Zartar Da Kudirin Dokar Yaki Da Shan Kwayoyin Kara Kuzari Ta Kasa


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Majalisar Dattawa ta zartar da dokar yaki da shan kwayoyin kara kuzari dake neman shigar da kudirin Hukumar Bunkasa Ilmi, Kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) akan yaki da shan kwayoyin kara kuzari tsakanin ‘yan wasa cikin dokokin Najeriya.

Majalisar Dattawan ta zartar da kudirin ne bayan data amince da rahoton da shugaban kwamitinta akan bunkasa wasanni da bangaren shari’a, hakkin dan adam da harkokin shari’a, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, ya gabatar mata akan kudirin yaki da amfani da kwayoyin kara kuzari na 2024.

Baya ga haka, kudirin na kuma neman a kafa cibiyar yaki da amfani da kwayoyin kara kuzari domin yaki da dabi’ar a tsakanin ‘yan wasa, domin dacewa da dokar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta duniya.

A watan daya gabata, Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya bukaci Majalisar Dattawan ta sake nazarin dokar.

Ya bayyana cewar hakan zai hana ‘yan wasa yin amfani da kwayoyin da zasu kara musu kwazo.

Bukatar Tinubun na kunshe ne a cikin wata wasikar da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Barau Jibrin ya karanta a zaurenta.

Shugaban Kasar ya kara da cewar kudirin zai samar da dokokin da zasu kai ga samar da Hukumar Yaki da Amfani da Kwayoyin Kara Kuzari ta Kasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG