Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar NDLEA Ta Kama Mahajjata Dauke Da Hodar Iblis A Legas


Hodar Iblis
Hodar Iblis

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun cafke wasu maniyyata hudu da suke shirin zuwa kasar Saudiyya dauke da hodar iblis a Legas.

Femi Babafemi, kakakin hukumar ta NDLEA ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Mista Babafemi ya ce jami’an hukumar NDLEA sun kai samame a otel din Emerald da ke Ladipo, Oshodi a jihar Legas a ranar 5 ga watan Yuni.

Hodar iblis
Hodar iblis

Ya ce an kama mahajjatan ne a yayin da suke kokarin hadiye hodar iblis din gabanin tashinsu zuwa kasar mai tsarki.

A cewarsa, wadanda aka kama a yayin samamen sun hada da Usman Kamorudeen mai shekaru 31, da Olasunkanmi Owolabi mai shekaru 46, da Fatai Yekini mai shekaru 38, da wata mace mai suna Ayinla Kemi mai shekaru 34.

Mutum biyu daga cikinsu da ake zargi suna shirin hadiye kunshi 100 kowannensu,” inji shi.

Shugaban NDLEA, Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya ce hukumar za ta ci gaba da bincike don ganowa da kuma kamo masu aikata laifuka, musamman wadanda za su iya fakewa a karkashin aikin hajji domin aiwatar da munanan ayyukansu da za su iya zubar da kimar kasar.

“Hukumar za ta yi aiki tare da takwarorinmu na Saudiyya don ganin an gano wadanda ke aikata wadannan haramtattun aikin a kowane yanki na Saudiya kuma a yi maganinsu yadda ya kamata,” inji shi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG