Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Na Neman Hanyar Dakile Amfani Da Wayoyi Wajen Aikata Ta’addanci


Taron yan Majalisa da Sanatocin Najeriya.
Taron yan Majalisa da Sanatocin Najeriya.

Tabarbarewar tsaro a Najeriya ya sa Majalisar Dattawa ta umarci kwamitin Sadarwa ya gaiyaci ministan Sadarwa, Dakta Ali Isa Pantami, domin a fahimtar da shi bukatar samar da mafita.

Wannan mataki da Majalisar ta dauka ya biyo bayan wani kudiri ne da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Sanata Emmanuel Bwacha ya gabatar a zauren Majalisar, inda ya nuna damuwa akan mummunan halin rashin tsaro da kasar ke ciki a halin yanzu.

Sanata Bwacha, ya ce a cikin Najeriya ne kawai za a iya amfani da kayayyakin sadarwa irin su wayar hannu ba tare da wani tsari na zamani ba. Ya kara da cewa yanzu haka yan fashi da yan ta'adda suna tattaunawa don neman kudin fansa ta hanyar amfani da wayoyi tare kuma da yin nasara.

Majalisar ta bukaci kwamitin Sadarwa da ya nuna wa Ministan bukatar aiwatar da kudurorin ta, game da al'amuran tsaro da suka shafi aikin ma'aikatarsa.

A cewar Sanata Abdullahi Adamu, duk wani mai hankali kuma dan kasa dole ne batun tsaro ya tayar masa da hankali domin ba wai ta hanyoyin sadarwa kawai ba, lamarin ya haifar da sace sacen mutane da fashi da makami da kisan gilla da ma sauran aiyukan ta'addanci a kasar, inda ya bada misali da yadda aka sace shugaban Jamiyyar APC a jihar sa ta Nasarawa, amma aka samu gawar sa a kusa da gidan sa washe gari.

Amma a wani abu mai kamar mayar da martani, Ministan Kula da ma'aikatar Sadarwa Isa Ali Pantami, ya bada bayanin cewa tun lokacin da ya kama aiki an rufe layukan waya sama da miliyan biyu, wadanda ba a yi rajistar su ba. Pantami ya ce akwai matakai da yake dauka akan rufe layuka da hana su aiki a kasa sai masu shi sun je sun yi masu rajista.

A yanzu dai Majalisa Dattawan ta ce ta damu ainun da yadda tsakanin masu bada kariya da wadanda ake karewa ke kara lalacewa a sakamakon karya doka da oda, kamar yadda aka nuna a lokacin zanga zangar ENDSARS wanda wasu bata gari suka kwace daga baya.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG