Tsoshon jakadan Najeriya a kasar Sudan, ambasada Suleman Dahiru ya bayyana cewa mai yasa a kowane lokaci ‘yan Afirka kadai wannan kotu ke tuhuma?, ya kara da cewa yayi ambasada a kasar Sudan kuma yasan da cewa anyi abubuwan da basu dace ba amma a cewar sa ba a sudan kadai irin wadannan abubuwa suka faru ba.
Tsohon ambasadon ya kara da cewa mai yasa a lokacin da aka yi rikici a kasar Bosniya turawan yamma basu yi komai ba!, mutanen da aka hallaka a Sudan lokacin rikicin Dafur basu kai yawan jama’ar da aka hallaka kokuma ake ci gaba da hallakawa a kasar Iraqi ba.
Barista Aliyu Abdullahi lauyan tsarin mulki a Najeriya ya bayyana cewa duk kasar data rattaba hannu ya kamata ta bi dokar wannan kotu, kuma kamar yadda mai shari’ar wannan kotu ya bada umurni ya kamata a bashi goyon baya koda wane shugaban kasa ne kuwa.
Ya kara da cewa abin da yasa kasashenmu na Afirka ke ja dabaya wajan irin wannan gayyata da ake wa wasu shugabanni na Afirka, sunga cewa akwai wasu shugabanni da suke wajen Afirka wadanda suka aikata abinda yafi abinda na kasashen Afirka suka aikata amma ba’a gurfanar dasu gaban kotun ba.
Daga karshe Baristan ya amsa tambayar da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Hassan Maina Kaina yayi masa cewa ko hakan ya dace? Sai ya kada baki yace “lallai bai dace ba, domin yakamata kotun ta hukunta kowane shugaban kasa daidai da saura.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.