Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kasar Falasdinu, duk da irin adawar da Amurka da Isra'ila suka nuna ga daukar wannan matakin.
A lokacin da yake jawabi ga Babban Zauren Taron majalisar Dinkin Duniya, bayan da zauren taro ya mike tsaye yana tafa masa, shugaban majalisar mulkin kan Falasdinawan ya bayyana kasar Isra'ila a zaman "mai mamaya" ya kuma ce rike yankunan Falasdinawa da take yi manufa ce ta tsugunar da 'yan mulkin mallaka a yankunan da ta mamaye.
Isra'ila ta yi adawa da shirin Falasdinawa na neman a amince da kasarsu a Majalisar Dinkin Duniya, tana mai cewa hakan ba zai ciyar da kokarin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya gaba ba.
Firayim ministan bani Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayarda shawara a cikin jawabinsa daga baya cewa a fara shawarwarin neman zaman lafiya nan take a majalisar idan har da gaske sassan suke yi kan cimma yarjejeniya. Ya sake jaddada matsayin Isra'ila cewa ba za a iya cimma zaman lafiya ta hanyar kudurorin Majalisar Dinkin Duniya ba.
Mr. Netanyahu ya dora ma Falasdinawa laifin kasa komawa ga shawarwarin neman zaman lafiya kai tsaye yana mai fadin cewa su a gare su babbar matsalar ba ita ce ta fadada unguwannin yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ba, matsalar ita ce Falasdinawa sun ki yarda su amince da kasar Isra'ila a zaman kasar yahudawa.