Isra’ila da kungiyar Hamas sun fara gudanar da shirinsu na musanyar fursunoni inda za a musanya daruruwan Falasdinawa dake kurkukun Isra’ila da wani sojan Isra’ila mai suna Gilad Shalit da aka kama.
Kwambar motoci dauke da Falasdinawan da za a sako yau talata sun taso daga gidajen kurkuku na Isra’ila zuwa tasoshin bakin iyaka kafin asubahin yau talata.
Yarjejeniyar musanyar ta tanadi sako Falasdinawa fursunoni su 477 a yau talata, yayin da za a sako karin 550 a cikin watanni biyun da ke tafe.
Ita kuma Hamas zata sako wannan sojan Isra’ila Gilad Shalit. Za a mika sojan na Isra’ila ga Masar wadda ita kuma zata mika shi ga Isra’ila a daidai lokacin da aka fara sako Falasdinawan.
A bayan sako shi, za a dauki Shalit zuwa wani sansanin mayakan sama inda firayim minista Benjamin Netanyahu da sauran shugabanni da kuma iyalansa zasu tarbe shi.
Daga cikin Falasdinawa 477 da za a sako yau talata, za a tasa keyar 100 zuwa yammacin kogin Jordan, za a kori kimanin 40 zuwa gudun hijira a Jordan da Turkiyya da Qatar da kuma Syria. Sauran kuma za a sake su su koma Gaza inda Hamas ta shirya musu tarba ta gwarzaye.