A taron da gwamnonin biyar John Kerry ya tsara hanyoyi da matakan da kasar Amurka zata dauka domin tallafawa jihohin su yaki talauci da rashin aikin yi.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal na cikin gwamnonin guda biyar da suka gana da Mr. John Kerry a fadar gwamnatin tarayya..
Aminu Tambuwal yace John Kerry ya kara jaddada goyon baya ga gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari musamman akan yakin da ta keyi da cin hanci da rashawa.
Gwamnonin sun tattauna da John Kerry akan matsalolin da suka shafi samun zaman lafiya a arewacin Najeriya da kuma sha'anin ilimi, musamman ilimin yara mata da harkokin kiwon lafiya da samarda wutar lantarki.
Allah ya ba arewacin Najeriya kafafe da dama da za'a iya anfani dasu a samu wutar lantarki mai araha. mai kuma dorewa, musamman idan aka yi anfani da hasken rana da kuma iska da kuma ruwa.
John Kerry yace gwamnatin Amurka zata shigo da karfinta ta bada goyon baya domin tabbatar da cewa an kara kyautata sha'anin wutar lantarki a arewacin Najeriya da ma kasar gaba daya.
Amurka ta fahimta cewa idan aka inganta rayuwar al'umma aka kuma samar ma mutane aikin yi matsaloli irin na tashin hankali zasu ragu matuka dalili ke nan da ya kamata Najeriya ita ma ta gane domin kasar ci moriyar taimakon.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.