WASHINGTON DC —
Watakila kafofin yada labarai a Najeriya sun yi bibiya kan dokar da aka kafa a wajajen karshen mulkin Shugaba Goodluck Jonathan, wato Cyber Crime Prohibition Act.
Wannan doka ita ta hana aikata laifi a shafukan internet ko kafofin sada zumunta.
A karkashin wannan dokar ce 'yansandan Najeriya suka kama Musa Azare da kuma wani Abu Saddiq, dukansu sanannun marubuta a internet.
Ga cikakken bayani akan wannan batun.