"Muna cikin wani sabon babi na ta'addanci a fadin duniya, inji mukaddashin sakataren ma'aikatar tsaron cikin gida Alejandaro Mayorkas, a bayani da yayi a gaban wani kwamitin majalisar dokokin Amukar jiya Alhamis.
"Saboda yanayin irin wadan nan hare hare da suka samo sarsala daga farfagandar ISIS, yana da wuya jami'an aikin leken asiri da dana tsaro, su gano su gabannin su kai hare haren, kuma hakan yana iya aukuwa ba tareda an sani ba," inji sakatare Mayorkas.
Dan majalisar dattijai Tom Carper na jam'iyyar Democrat, yace ya amince da matsayar hukumar tsaron cikin gidan, ya bada misali da harin da aka kai a San Barnerdino jihar California, da maharan suka halaka mutane 14.
Daga Iraqi kuma, rahotanni sun ce mazauna birnin Fallujah wadanda suke arcewa daga zazzafar bata kashin da ake yi tsakanin mayakan sakan ISIS da dakarun Iraqi, suna cikin halin "dimuwa," saboda tsananin amon wuta, da kuma matsanancin 'yunwa da suka shiga.