A jamhuriyar Nijer kamar sauran kasashen duniya ana ci gaba da gabatar da azumin watan Ramadan sai dai kuma ana cikin yanayin tsananin zafin rana. Wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ya zazzagaya lungunan birnin ya hada ma na rahoto kan yadda ya ga azumi na gudana.
Kasar dai ta Nijer na daya daga cikin kasashen dake fama da tsananin zafin rana a wannan watan, kuma baicin hakan, mutane na kukan rashin kudi.
Sai dai kuma wadanda Allah Ya huwacewa na yin abincin buda baki fiye da kima, su kan ci har su zubar. Wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ya ce kullum safiya sai an ga abinci a tule a bakin titi, ko a bola ko cikin ruwan gwalalo.
Malaman addinin Islama na kasar ta Nijer su na ta fadakarwa tare da jan hankulan jama'a su guji bannar abinci da almubazzaranci.