Ma’aikatan ceto na ta faman kokarin cimma wasu wurare cikin tsaunuka a Pakistan da Afghanistan da girgizar kasa mai karfin 7 da digo 5 na ma’aunin rikta ta auku a kasasehn.
Ta hallaka akalla mutane 360 da raunata fiye da 2,200 a tsakanin kasashen biyu. Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya fada a shafinsa na Twitter a jiya Talata cewa, yawan mamatan kasarsa ya karu zuwa 115.
Sai kuma wadanda suka jikkata da suka kai akalla mutane 518 a yankuna 9 na kasar ta Afghanistan. Mutuwar ta hada da wasu ‘yan mata dalibai su 12 da aka tattake su garin gudu.
Lokacin da suke kokarin ficewa daga gine-ginen da ke layin Faduwa a Lardin Takhar. Masu aikin agaji sun ce taimakawa dukkan wuraren da girgizar kasar ta shafa zai dauki lokaci.