Jiya Litinin aka samu wata girgizar kasa a Afghanista wadda ta kai karfin 7.5 a ma'auni rikta har ta kai kasar Pakistan.
Kawo yanzu girgizar kasar da ta faru a arewacin Afghanistan ta yi sanadiyar mutuwar mutane 300 tare da raunata mutane fiye da 1,700.
Bayan girgizan sassan duniya daban daban suka dinga bada tayin taimako jiya da yamma jim kadan bayan aukuwar girgizar.Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace hukumomin majalisar suna tattara kaya domin su kaiwa gwamnatin Afghanistan taimako musamman ga wadanda abun ya rutsa dasu a Afghanistan da Pakistan idan har an bukaci su yi hakan.
Mai magana da yawun Majalisar Stephane Dujarric tace rahotanni da suke shigowa sun nuna akwai hasarar rayuka da yawa da rugujewar gine gine a kasashen biyu, wato Afghanistan da Pakistan.
Yace Mr Ban ya mika ta'aziyarsa da juyayi ga gwamnatoci da al'ummar kasashen Afghanistan da Pakistan musamman wadanda suka rasa 'yanuwa da abokai.
A Amurka kakakin Fadar White House Josh Earnest yace kasar ashirye take ta taimakawa gwamnatocin Afghanistan da Pakistan.
A Indiya Firayim Ministan ksar Narendra Modi ya kira Ashraf Ghani na Afghanistan ya bada taimako.
Kasar Iran ma tace ashirye take ta tura jami'anta na bada agajin gaggawa wurin ceto wadanda girgizar ta rutsa dasu.