Kungiyar ma’aikatan Kiwon Lafiya a jihar Bauchi, sun fara wani shiri na shiga yajin aikin sai wanda ya gani. Inda suka bai wa Gwamnatin Jihar makonni biyu don su cika alkawalin da suka cimma a tsakanin kungiyar da kuma gwamnatin.
Idan hakan bai samu ba kuwa, za su umurci mambobin su da su fara yajin aiki, su kaurace wa duk wasu asibitocin gwamnati. Sun kara da cewar 'ya'yan kungiyar tasu na gudanar da ayyukan jinkai a fiye da cibiyoyi dubu daya, inda suke gudanar da ayyukan Kiwon Lafiya.
A taron 'yan Jarida da su ka gudanar a daya daga cikin cibiyoyin gudanar da ayyukan lafiya, Shugaban kungiyar, Kwamrade Yusuf Aliyu Fada, ya ce a dalilin halin kunci da 'ya’yan kungiyar tasu ke fuskanta, ya sa dole su gabatar da wannan bayanin da kuma neman mahukunta su kalli su da idon rahama, domin kuwa sun kwashe gomman shekaru suna aiki amma ba a basu koda sisin kwabo ba.
Kwamrade Yusuf ya kara da cewar, a duk lokacin da suka yi alkawali da gwamnati, ba a cika musu alkawalin, don haka su ke bukatar wannan karon ya zama lokaci da za a kyautata rayuwar ma'aikatan kiwon lafiya a jihar.
A hannu daya kuwa, Kwamishinan Lafiya na Jihar ta Bauchi, Dr. Samaila Dahuwa, ya bai wa 'yan kungiyar hakuri, da kuma basu tabbacin mika koken su zuwa ga Gwamnan Jiha. Kana ya tabbatar da cewar gwamnati a shirye ta ke ta dauki karin ma'aikatan kiwon lafiya, da kuma inganta rayuwar wadanda ke cikin aikin a yanzu.
Don bukatar sauraron rahoton Abdulwahab Muhammad a cikin sauti, sai a danna wannan.