A jahar Bauchi ma’aikata da kuma 'yan fensho suna cikin yanayin rudani da kuma rashin tabbas dangane da batun biyansu albashi da kuma hakkokinsu da ke wurin gwamnati mai shirin barin gado, ana kasa da makonni uku su mika mulki wa sabon gwamnati mai shigowa.
Ma’aikatan sun bayyana cewa wasu daga cikinsu sun fara yin bara da kuma bin kan 'yan uwa don yin maula da a yanzu haka ya jefa su cikin halin tsaka mai wuya.
Bincike na nuna cewa ma’aikatan da kuma masu karbar fensho a jahar Bauchi suna bayyana fargabar sake faruwar abin da ya faru a farkon kama mulkin wannan gwamnati mai barin gado, inda aka bar ma ta bashin albashin ma’aikata na tsawon watanni uku.
To saidai inji cewar mai fashin baki kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago a jahar ta Bauchi comrade Abdullahi koli, rashin biyan albashin ya janyo zargin jami'an gwamnati mai barin gadon da cewa sun yi amfani da kudaden ne domin biyan kansu alawus na barin aiki.
Shima gwamna mai shirin karbar mulki a jahar Bauchi, ta bakin kakakinsa Dokta Ladan Salihu, ya ce ya bukaci gwamnati mai barin gadon da ta biya ma’aikata hakkokinsu saboda gaza biyan kudaden zai kawo musu matsala da su ma’aikatan jahar.
Ga wakilinmu Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:
Facebook Forum