Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

London Na Shirin Gangamin Kin Amincewa Da Zyarar Donald Trump


Shugaban Amurka Donald Trump da Magajin birnin London, Sadiq Khan.
Shugaban Amurka Donald Trump da Magajin birnin London, Sadiq Khan.

Magajin birnin London babban birnin Birtaniya ya amincewa wasu dake son yin gangamin kin amincewa da ziyarar Shugaba Trump a ranar 13 ga wanna watan su gudanar da zanga zangar

Magajin Garin London ya amince da bukatar wasu masu zanga-zanga ta su saki wani balam-balan mai siffar Shugaban Amurka Donald Trump a fusace, saye da kamfai tamkar dan bomboi, yayin da Shugaban na Amurka zai kai ziyara a London, babban birnin kasar Burtaniya.

Balam-balam din mai tsawon mita 6 zai bi ta kan ginin Majalisar Dokokin Burtaniya da misalin karfe 9:30 na safe agogon yankin, a ranar 13 ga watan Yuli da za a yi zanga-zangar.

"Magajin Garin na goyon bayan zanga-zangar lumana tare kuma da sanin cewa hakan na iya haifar da wani abu,"

a cewar ofishin Magajin Garin na London Sadiq Khan a jiya Alhamis.

Leo Murray, dan rajin da ya jagoranci kirkiro balam-balam din, wanda ake wa lakabi da "Trump Dan Bomboi," ya yi amfani ne da kafar internet wajen tara kudi dala dubu ashirin wajen gina, abin da ya kira, "balam-balam dinmu mai tsawon mita 6 kuma mai ruwan doruwa mai siffar dan bomboi mai mugunyar fuska da guntayen yatsu, wanda zai bi ta kan tsakiyar birnin London yayin da Trump ke kai ziyara."

A yayin ziyarar ta tsawon kwanaki uku. Trump zai gana da Sarauniya Elizabeth da Firayim Minista Theresa May.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG