An ci gaba da gudanar da zanga zangar adawa da wata sabuwar doka a duk fadin kasar Poland, wacce ta yi sanadiyar Alkalan kotun kolin kasar uku suka sauka daga mukamansu.
Lech Walesa, wanda ya taba lashe kyautar Nobel, na daya daga cikin wadanda suka yi tattaki a birnin Warsaw a jiya Laraba.
Yayin kuma wani jawabi da ya yi ga gangamin masu zanga zangar a kofar kotun kolin kasar, ya jaddada kiran cewa lallai sai masu ra’ayin mazan jiya, sun sauka a mukamansu.
A cewar Walesa “duk wanda ya karya dokar kasar da tsarin yadda aka raba ayyukan gwamnati, to ya zama babban mai laifi, ya kuma zama dole mu yi iya bakin kokarinmu, mu ga cewa mun kori kowane ne, domin mu zabi wasu mutane daban.”
Ya kuma yi hasashen cewa, akwai yiwuwar irin matakin da gwamnatin ke dauka, ka iya haifar da yakin basasa a kasar ta Poland.
A jiya Laraba, Firai Ministan kasar Matuesz Morawiecki, (MATEWUSH MOROWIKKI) ya kare matakin da ya dauka a gaban majalisar tarayyar turai na rage shekarun da ya kamata Alkalai su yi ritaya daga mukamansu.
Facebook Forum