‘Yan tawaye da ma’aikatan kiwon lafiya a Libya, sun ce fada kusa da birnin Misrata dake hanun ‘yan tawaye, a yammacin kasar, ya kashe akalla mutane tara ya jikkata wasu hamsin.
Jami’an suka ce sojoji dake biyayya ga shugaba Moammar Gadhafi, sunyi amfani da bindigogin atilari yau lahadi, wajen fatattakar garin Dafniya,dake yammacin Misrata.
Wan nan fadan yazo a dai dai lokacin da jami’an Libya suka ce kungiyar tsaro ta NATO, ta kai hari kan wata unguwar gidajen kwana a yau lahadi, har ta kashe akalla farar hula tara, cikinsu har da yara.
NATO tace tana binciken ikirarin na Libya.
An kai ‘yan jarida gundumar Arada dake birnin Tripoli inda ake tafiyar da aikin ceto a wani gine da ake zargin harin ya rusa.
Mukaddashin ministan harkokin wajen Libya Khaled Kaim ya zargi NATO cewa da gan gan ta auna hari kan gidajen farar hula. Yace harin alamace ta “rashin imanin kasashen yammacin Duniya”.
Haka kuma hukumomin kasar sun kai manema labrai asibiti inda aka gwada musu gawarwaki da dama, ciki har da na yara kanana biyu,wadanda jami’an kasar suka ce harin na NATO ne ya halaka su.
Babu wata kafa mai zaman kanta da ta gaskanta wan nan ikirari.