PM Masar ya bayyana sha’warsa na ganin an jinkirta zaben ‘yan majalisar dokokin kasar har da aka ayyana za a yi cikin watan Satumba, har sai an kammala rubuta sabon tsarin mulkin kasar.
Essam Sharaf, yace duk da bayyana sha’awarsa, gwamnatin rikon kwariyar kasar zata yi bakin kokarinta na ganin an gudanar da zabe sahihi, koda yaushe aka kaddamar da shi.
Kalaman Mr. Sharaf sun zo ne a dai dai lokacin da ake kara samun masu korafe korafe daga kungiyoyin ‘yan ba ruwana cewa idan aka yi zaben cikin watan satumban, hakan zai fi taimakawa ‘yan kungiyar Muslim Bortherhood.
Wasu suna bayyana fargabar cewa majalisar dokokin kasar da ‘yan Muslim Borhterhood suke da rinjaye, zata kai ga tsarin mulki mai zubin addini.
Kungiyar Brtoherhood cikin watan mayun bana ne ta bada sanarwar kafa sabuwar jam’iyya da ta lakabawa sunan FJP a takaince ko Freedom and Justice party a turance. Kakakin jam’iyyar yace suna burin takarara kamar rabin kujeru dake majalsiar dokokin kasar.