Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyoyi Sun Nemi Australia Ta Hana Burtaniya Mika Assange Ga Amurka


Editar Wikileaks, Kristinn Hrafnsson, da Barrister Jennifer Robinson suna magana da manema labarai a karshen makon da ya gabata
Editar Wikileaks, Kristinn Hrafnsson, da Barrister Jennifer Robinson suna magana da manema labarai a karshen makon da ya gabata

Firai Ministan Australia, Scott Morrison, ya ce Assange ba zai samu wata kulawa ta musamman ba, inda ya ce, za a ba shi taimako ne, gwargwadon irin wanda za a ba kowanne dan kasar Australia da ya tsinci kansa a irin wannan lamari.

Lauyoyin daya daga cikin shugabannin kamfanin kwarmata bayanan sirri na Wikileaks, Julian Assange, sun yi kira ga hukumomin Australia, da su saka baki domin kada Burtaniya ta mika shi ga Amurka domin ya fuskanci tuhuma.

Amurka na son a tuso keyar Assange zuwa kasarta ne, domin ta tuhume shi kan irin rawar da ya taka a wani kwarmata bayanan sirri da aka jima ba a ga irinsa ba, wanda ya auku a shekarar 2010.

Assange, wanda dan asalin kasar ta Australia ne, zai fuskanci tuhuma ne kan zargin kutsen da ya yi a kwamputocin Amurka.

Idan kuma har aka same shi da laifi, zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na tsawo shekaru biyar, sannan akwai yiwuwar masu shigar da kara su kara mai wasu tuhume-tuhume a nan gaba.

Sannan kasar Sweden ma ta ce tana duba yiwuwar tuhumar shi, kan wani zargin aikata fyade.

Sai dai Firai Ministan Australia, Scott Morrison, ya ce Assange ba zai samu wata kulawa ta musamman ba, inda ya ce, za a ba shi taimako ne, gwargwadon irin wanda za a ba kowanne dan kasar Australia da ya tsinci kansa airin wannan lamari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG