A cewar Farfesa Samuel Zalanga, rashin tafiya da matasa a harkokin tafiyar da kasa zai iya haifar da rashin jituwa.
“Mafi yawan mutanen da ke Najeriya matasa ne, kuma matasan ba aiki su ke da shi ba, wasu masana suna kiran matasan da ke Afrika wani yayi da ake kira “jirantaka”, wato suna jira sun gama makaranta amma babu aiki.” In ji Farfesa Zalanga.
Wannan a cewarsa, babban abin damuwa ne domin zai iya janyo sa-in-sa.
Dangane da matakan da gwamnati ya kamata ta dauka wajen kawar da matasan daga sha’awar shiga ayyukan da ba su dace ba. Farfesa ya ce batun samar da ayyukan yi ya kamata a fi maida hankali fiye da karatu.
“Samawa matasa aiki, ya fi mahimmanci game da zancen karatin domin ko sun yi karatun ba su da aiki, ya kan rage musu mutuncin karatun.” A cewar Zalanga.
Saurari Cikakkiyar Hirar A Nan: