Manufar sabuwar kungiyar ta Junde Jam Fulani Association of Nigeria itace hadin kan matasa domin yin tafiya daidai da zamani da kuma kwato wa Fulani hakinsu.
A cewar shugaban sabuwar kungiyar Abdullahi Maikano kungiyar zata dukufa wajen hadin kan matasa ne.Yace babu wani mutum dake da hankali da zai goyi bayan kisa ko sata. Rashin shugabanci nagari ya hana a kira matasan a tsayar da magana daya. Sai an san abun dake faruwa kafin a ce za'a dauki mataki.
Mataimakin kungiyar Abdulkarim Bayero yace zasu hada kan matasa domin mika korafinsu ga gwamnati. Zasu wayar wa matasansu kai ta fannin ilimi. Dangane da sace sacen shanu da suka haddasawa Fulani hasarar dukiyoyinsu, yana son gwamnati ta taimaka ta rage masu hasarar.
Muhammad Lawal Ardo Haruna yace cigaba ne a samu kungiyoyi da dama. Kungiya daya ba zata wadatar da bukatun Fulani ba. Yawansu shi ya fi a'ala.
Tsohon shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen Filato Inusa Jibrin Jagaba ya ba sabuwar kungiyar shawara. Yace su kasance masu da'a da sanin yakamata. Su dinga kiran matasa saboda su san abubuwan dake faruwa.
Ga karin bayani.