Sai dai kuma wani bayanin da aka buga a shafin Bill da Malinda Gates a kan intanet na nuni da cewa yau shekaru biyu da watanni ke nan ba a samu kaiwa ga yara su dubu 165 ba a wuraren da ake tashin hankali a yankunan Blue Nile da Kordofan ta Kudu a kudu maso gabashin kasar Sudan. A yanzu yaran yankin su na cikin kasadar kamuwa da wannan cuta ta Polio wadda zata iya nakkasawa kamar yadda bindigogi ke nakkasa jama'a.
Sai dai kuma babban abinda ya bayarda kwarin guiwa shi ne cewa a makon da ya shige, an samu kaiwa ga yara miliyan 7 wadanda aka diga wa maganain rigakafin polio a kasar ta Sudan.
Kwararru sun ce ba zasu yi kasa a guiwa ba, ba zasu bar rikice-rikice su ja musu burki ba. Suka ce a shirye suke domin kaiwa ga kowane yaro a inda duk ake rikici.