Hade ma’aikatar ayyuka da gidaje da makamashi wurin guda karkashin Minista daya na ci gaba da jan hankalin kwararru a Najeriya.
Tsohon Gwamnan jihar Lagos, Babatunde Raji Fashola, aka durawa alhakin tafiyarda wannan bangare.
Korarrun Inginiyoyi irinsu Manu Ibrahim, na da kwarin gwiwar cewa fashola ka iya cire kitse daga wuta. Yana mai cewa kasancewar Fashola yayi abun tasiri a jihar Lagos ai kaga yanzu an kara fadadamasa.
Ya kara da cewa babban kalubale ne ke gareshi kuma aikin ne da yake bukatar hannu dayawa daga kowane fani.
A daya bangare kuma nadin da aka yiwa dan jarida Adamu Adamu, a matsayin Ministan Ilimi da kuma Farfesa Anthony Onwuka, a matsayin karamin MInista shima masu sharhi na kalon abun ta mahanga daban daban.
Jafar Jafar wani dan jarida dake Abuja ya ce Farfesa Onwuka, kwararren malami mne na makaranta a harkar ilimi shi gangaran ne Adamu Adamu shima kwararre ne a harkar jarida amma gaskiya a tsari na aiki bai dace asa wanda ikai matsayin Farfesa a saman Farfesa.