Daga cikin bukatun da Cameron ya gabatar, akwai batun samar da kariya ga kasashen nahiyar da yawansu ya kai kashi daya cikin uku, wadanda ba sa amfani da kudin bai-daya na Euro.
Cameron ya kara da cewa, idan har, nahiyar za ta koma amfani da kudin na bai-daya baki dayanta, to Burtaniya ba ta cikin wannan tsari.
Ya kuma tabo batun cewa a samar da wani tsari da zai baiwa kasashen nahiyar damar kin amincewa da dokokin kungiyar da ba sa kare hakkokinsu.
Firai ministan na Burtaniya ya kara da cewa, yana goyon bayan tafiye-tafiyen ma’aikata a tsakanin kasashen, amma ya ce akwai bukatar gwamnatocin su samu karfin fada a ji, musamman kan batutuwan da suka shafi bakin haure.
2