Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya tabbatar wa magoya bayan Liverpool a ranar Litinin cewa tattaunawar da aka yi kan kwantiragin tauraron dan wasan gaba Mohamed Salah "abu ne da aka saba" bayan da alama ‘dan kasar Masar din ya yi kira ga kungiyar ta warware matsalar.
“Kun san ainihin matsayin sa kuma muna magana da sauransu , tsawaita kwantiragi na ‘dan wasa kamar Mo (Salah) ba abu ne da kuke yi ba (lokacin da kuka hadu shan shayi da rana ku tsaida yarjejeniya ba). Wannan al'ada ce gaba ɗaya, babu wani abu da za a ce game da Mo. Yana magana game da kanshi idan an tambaye shi game da shi."
"Zan iya tsokaci kadan kawai saboda duk sauran abinda za a bayyana a fili ba ne. Amma ban tabbata ko ya yi hirar da Turanci ba ko kuma an fassara ta (ba daidai ba) daga Larabci zuwa Turanci kuma wannan babban batu ne yadda muka sake gani a kwanakin baya. Don haka, hakika abubuwa da yawa na iya faruwa idan wani ya yi ƙoƙarin yin hakan. Mo bashi da damuwa. Ni ma bani da damuwa. Ina tsammanin abin da muke so a bayyane yake kuma abubuwa kamar wannan suna buƙatar lokaci. Shi ke nan,” in ji kocin Liverpool, Jurgen Klopp.
A wata hira da gidan talabijin na MBC Masr TV na Masar, an ambato Salah mai shekaru 29 yana cewa, "Na fadi hakan sau da yawa, idan shawarar ta taso, ina so in ci gaba da zama a Liverpool."
Salah ya kara da cewa, "Amma hukuncin yana hannun mahukunta kuma dole ne su warware wannan batu."
Dan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar Premier a yanzu (13) yana karkashin kwantiragi a Anfield har zuwa lokacin bazara na 2023.