A birnin Moscow, wani shagon sayar da sutura na sojin Rasha ya sa hoton Trump a wani katafaren akwatin wuta na tallace tallace, inda ya kuma tallata yiwa Amurkawa rangwame.
Trump ya bayyana karara a jawabinsa bayan rantsuwa cewa, gwamnatinsa zata bada fifiko wajen biyan bukatun Amurkawa.
Shekara da shekaru mun yi ta azurta masana’antun kasashen ketare a maimakon na Amurka, muka rika tallafawa rundunonin sojin wadansu kasashe, muna rage yawan dakarunmu a cikin gida, mun kare iyakokin wadansu kasashe yayin da muka ki kare namu.
A Afirka ta yamma, ra’ayoyi sun banbanta a Najeriya da Nijar. Amurkawa sun yabawa gwamnatin Barack Obama, muna yi masa addua, muna addu’a ga shugaba Donald Trump fatar Alheri a gwamnatinsa, a cewar Mallam Bello daga Nijar.
Duk da zafafan kalaman yakin neman zaben Trump, a cikin shekara guda da ta shige, addu’armu gareshi itace ya yi kokari ya hada kan kasashen duniya. Muna kuma fatar zai taimaki kasashe masu tasowa su habaka, a cewar wani ‘dan Najeriya.
Bukin rantsarwar ya samu halartar Amurkawa da kuma al’umman kasashen duniya da dama.