A karo na biyu kwamitin binciken gano adaddin asarar rayuka da kuma dukiyar da aka yi a yankin Mambilla sakamakon tashe tashen hankulan da aka yi a watannin baya da gwamnatin jihar Taraba ta kafa, ya kammala zamansa a Gembu na karamar hukumar Sardauna.
A wannan karon kwamitin ya tantance sunayen magada ne domin samun alkalumman wadanda aka kashe domin samun tallafi daga gwamnatin jihar.
Ambassada Emmanuel Njuwa shine shugaban wannan kwamitin. Yace sun hada rahotonsu kuma sun mikawa gwamnan jihar wanda zai yanke shawara akan irin taimakon da zai bayar
Wani mutum mai suna Bello wanda aka kashe dan’uwansa yace an dauki sunayen su, tare da alkawarin cewa gwamnati zata taimaka. Ita m wata mace mai Amina Saidu wanda mijinta lauya ne da aka kashe a rikicin Anguroji dake tsaunin Mambila ta ce ya barta da ‘ya’ya shida tayi farin ciki da taimakon da gwamnati zata bata.
Alhaji Umaru Zubairu, wakilin Mambila, ya ce abun da gwamnati ta yi abun godiya ne.
To sai dai kuma wasu na ganin akwai abun dubawa. Alhaji Bakari Muhammad Tamniya wani dan asalin yankin Mambila ya bada shawarar cewa kafa kwamiti yayi daidai, amma da wakilan kwamitin su kasance wasu daga wurare daban ne.
Yayin da kwamitin ke kammala aikinsa, wata sabuwa kuma ta kunno a yankin Yorro inda jami’an tsaro ke binciken kisan gillar da wasu matasan Mummuye suka yiwa wasu Fulani shida, batun da masarautar Mummuye dake tutiyar samun zaman lafiya ke cewa dole a yi bincike, domin hukunta mai laifi.
Saurari Rahoton Ibrahim Abdulaziz don jin karin bayani
Facebook Forum