Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwamitin Duba Zargin Cin Zarrafi Da Kisan Gillan Masu Zanga-Zangar ENDSARS A Lekki Ya Saba Ka’ida - Keyamo


Zanga Zangar #ENDSARS
Zanga Zangar #ENDSARS

A yayin da ake dakon farar takardar rahoton kwamitin duba zargin kashe masu zanga-zangar ENDSARS a Lekki, karamin ministan kwadago, Festus Keyamo, ya caccaki kwamitin da aka kafa domin binciken laifukan cin zarafi da kisan gilla da ake yiwa 'yan sanda a zanga-zangar ENDSARS.

Keyamo ya bayyana hakan ne a yayin amsa tambaya a cikin shirin "Siyasa a yau" na gidan talabijIn na Channels kan matsayin gwamnati musamman dangane da rahoton da kwamitin da aka kafa a Legas ya fitar, inda ya bayyana kwamitin a matsayin wanda a ka kafa ba bisa ka’ida ba.

Keyamo ya ce a matsayinsa na babban lauya mai mukamin SAN da hakki da ya rataya a wuyansa da kuma ra’ayinsa, kwamitin ya sabawa ka’ida.

Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan fitowar rahoton kwamitin wanda ya tabbatar da zargin harbin masu zanga-zanga da ake yiwa jami’an sojojin Najeriya da na ‘yan sanda, inda rahoton ya ce hakika jami’an tsaron sun harbe masu zanga-zangar da ba su dauke da wani makami.

A yayin da har yanzu ba a fitar da rahoton a hukumance ba amma aka yi ta ganin jita-jitar sakamkon rahoton a kafaffen sada zumunta, inda kwanaki bayan haka kwamitin ya mika sakamakon bincikensa ga gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas.

Daya daga cikin ababen da rahoton ya tabbatar akwai zargin cin zarafi da ‘yan sanda suka yi yayin da dayan kuma na kan harbe-harbe a unguwar Lekki da ke jihar Legas a ranar 20 ga Oktoba shekarar 2020 kamar yadda rahoton da ake yadawa a kafaffen sada zumunta ya nuna.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta yin harbi kai tsaye kan masu zanga-zangar.

A ci gaba da kokarin sanin tushen lamarin, gwamna Babajide Sanwo-Olu a ranar Litinin ya kafa wani kwamiti mai mutane hudu karkashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Legas mai mukamin SAN, Moyosore Onigbanjo, domin gabatar da farar takarda na musamman kan rahoton zargin harbi da cin zarrafin masu zanga-zanga a Lekki.

Ana dai sa ran nan zuwa kasa da kwanaki biyu kwamitin da gwamna Sanwo-Olu ya kafa zai mika shawarwarinsa ga hukumar kula da tattalin arzikin kasa wato NEC domin tattaunawa da yiwuwar aiwatar da shi shawarwarin ciki.

XS
SM
MD
LG