Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

#EndSars: Tabbas Sojoji Sun Kashe 'Yan Gangami a Kofar Lekki- Kwamitin Bincike


Zanga Zangar #ENDSARS
Zanga Zangar #ENDSARS

Kwamitin da gwamnatin jihar Lagos ta kafa domin bincike hargitsin da ya biyo bayan zanga-zangar lumana ta #EndSars ya tabbatar da cewa, jami'an tsaro sun kashe masu zanga zanga da dama a kofar Lekki.

Kwamitin da ya yi zama karkashin mai sharia'a Doris Okuwobi ya gano cewa, Sojoji sun yi harbin kan mai uwa da wabi a inda masu zanga zangar da galibi matasa ne da ke zanga zangar nuna alhininsu kan yadda 'yan sanda su ke muzguna masu, sau da dama kuma su tuhume su da aikata miyagun laifuka ba tare da hujja ba galibi domin ganinsu dauke da komfutar tafi da gidanka-laftop ko kuma sanya sutura ta 'yan zamani.

Kwamitin binciken zanga zangar #EndSars
Kwamitin binciken zanga zangar #EndSars

A rahoton mai shafi 309, Kwamitin ya bayyana yadda jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda da kuma sojoji su ka wuce gona da iri wajen gudanar da aikinsu, inda su ka yi amfani da karfin bindiga kan masu zanga zangar lumana da basu dauke da makamai, abinda ya saba wa ka'idar aikinsu. Kwamitin ya kuma tabbatar da cewa, sojojin sun kashe mutane da dama su ka kwashe gawarwakin da kuma harsasan da suka yi amfani da su domin boye laifin.

Wani bangaren rahoton ya bayyana cewa, “ Kwamitin na musamman ya gano cewa, ranar 20 ga Oktoba, 2020 a kofar Lekki, jami’an sojojin sun yi harbi suka kuma kashe masu zanga zanga da basu dauke da makamai ba gaira ba dalili, lokacin suna dauke da tutar Najeriya suna raira taken Najeriya, kuma za a iya bayyana irin yadda aka kai masu harin aka kuma kashe su a matsayin kisan kiyashi.”

Shugabar Kwamitin binciken zanga zangar #EndSars Alkali Doris Akuwobi
Shugabar Kwamitin binciken zanga zangar #EndSars Alkali Doris Akuwobi

Raboton ya kuma ci gaba da cewa “Kwamitin binciken na musamman ya gano cewa, abinda Rundunar Sojin ta aikata ya kara muni ta wajen hana motocin jinyar gaggawa taimakawa wadanda su ke bukatar jinya. Haka kuma Rundunar Sojin ba ta sabawa ka’idar gudanar da aikinta a yanayi irin wannan."

Kwamitin ya bada umarni a biya mutane 70 wadanda rundunar 'yan sandan SARS suka ci wa zarafi diyyar Naira Miliyan 410 daga cikin mutane 235 da kwamitin ya saurari korafe-korafensu. Bisa ga rahoton kwamitin, 14 ne kadai daga cikin dumbin wadanda aka saurari korafe-korafensu su ka shafi harin kofar Lekki da jami'an tsaro su ka kaiwa masu zangar zangar #EndSars.

A hirar shi da Muryar Amurka, matashin da ya shirya gangamin Temitope Oanu Majek Davis wanda kuma ya ke daya daga cikin membobin kwamitin binciken na musamman ya bayyana cewa, ya fara tada tsimin matasa ne su hada kai su kai korafinsu gaban hukumomi a jihohinsu da nufin jawo hankalin shugaban kasa ya dauki matakin kawo karshen cin zarafin al'umma musamman matasa da rundunar 'yan sanda ta SARS ke yi. Ya kuma bayyana cewa, duk da yake sun yi asarar rayuka bayan da bata gari suka shiga cikinsu suka rika tada hankalin al'umma, hakar gangamin ta cimma ruwa domin duniya ta fahimci irin keta doka da wuce gona da iri da wannan runduna ke yi, da ya kai ga soke ta.

Matashin da ya shirya zanga zangar #EndSars Temitope Oanu
Matashin da ya shirya zanga zangar #EndSars Temitope Oanu

Muryar Amurka ta kuma yi hira da wadansu da suka gabatar da korafe-korafe gaban kwamitin binciken a jihar Lagos wadanda 'yan sandan SARS suka ci zarafi da ko dai su ka yi sanadin rasa kaunatattunsu, ko rashin lafiya da ya nakasa su, ko rasa ayyukansu, da dai sauransu.

Wani da ya kai korafi gaban kwamitin binciken zanga zangar #EndSars
Wani da ya kai korafi gaban kwamitin binciken zanga zangar #EndSars

Daya daga cikin wadanda Muryar Amurka ta yi hira da shi ya bayyana yadda wani da suka sami sabani a wurin aiki ya hada baki da jami'an SARS aka yi mashi kage da ya kai ga rasa aikinshi da kuma kwace dukan kaddarorinsa.

Wani da jami'an tsaron SARS suka gasawa akuba
Wani da jami'an tsaron SARS suka gasawa akuba

Idan za a iya tunawa, gwamnan jihar Lagos Babajide Olusola Sanwo-Olu ya kaddamar da kwamiti na musamman mai mutane bakwai a ranar 19 ga watan Oktoba, 2020 domin gudanar da bincike da kuma bada shawarwari kan yadda za a shawo kan matsalar, da zai kai ga zaman lafiya a jihar, da kuma samun yarda tsakanin matasa.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Lagos Gbenga Omotoso
Kwamishinan watsa labarai na jihar Lagos Gbenga Omotoso

Bayan karbar rahoton kwamitin nan da nan gwamnan jihar ya kafa kwamitin mutane hudu karkashin jagorancin babban Atoni Janar na jihar Moyosore Onigbanjo (SAN) da zai tabbatar da aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Tuni wadansu lauyoyi su ka yi barazanar fitar da cikakken rahoton kwamitin a bainin jama'a idan gwamnatin jihar Lagos ba ta cika alkawarinta na aiwatar da shawarwarin da kwamitin binciken ya bayar ba.

yadda-aka-gudanar-da-zanga-zangar-endsars-a-legas-abuja

wasu-sojojin-najeriya-sun-tsare-ma-aikaciyar-voa-a-port-harcourt

masu-zanga-zangar-end-sars-sun-cancanci-yabo---minista-sunday-dare

endsars-yan-sanda-sun-zubawa-matashi-fetir-a-baya-suka-cinna-mashi-wuta-a-binuwe

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG