Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a fadar Aso Rock da ke Abuja, yayin da ya karbi bakuncin Mista Antony Blinken, sakataren harkokin wajen Amurka.
Akasarin gwamnatocin jihohi da ke cikin lamarin sun ba da sharudda daban-daban game da kwamitin binciken kamar yadda mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina ya ruwaito shugaban yana cewa, sai bayan matakan da gwamnatocin suka dauka gwamnatin tarayya zata shiga lamarin.
Gwamnatin tarayya na jiran matakan da jihohi zasu dauka, kuma za ta bar gwamnatocin jihohin da lamarin ya shafa su bi tsarin da suka fitar ya yi aiki sannan idan da bukata gwamnatin tarayya ta shigo ciki zata shiga, inda gwamnatin tarayya ke cewa ba za ta iya tilasta musu ra'ayoyi ba kuma dole ne gwamnatin tarayya ta jira martanin jihohin in ji Femi Adeshina.
Tuni dai yan Najeriya musamman wadanda suka shirya zanga-zangar ENDSARS kamar su DJ Switch, mawaki Falz suka fara tofa albarkacin bakin su a game da nasarar da rahoton ya fitar na cewa sojojin Najeriya sun harbi wasu daga cikin masu zanga-zangar har lahira.
Shi ma babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, ya bayyana cewa sai an mikawa rundunar tsaron kasar rahoton a hukumance kuma ita rundunar ta fitar da sanarwar farar takarda wato white paper kafin ya yi jawabi a kai inda ya gargadi yan kasar da su gujewa fadin ababen da bai kamata ba da ka iya tunzura jama’a a game da lamarin kafin rundunar tsaro kasar ta yi magana.
Rahoton kwamitin da aka kafa a jihar Legas dai ya yi nuni da cewa tabbas an rasa rayuka a Lekki Toll gate na jihar a yayin zanga-zangar na ENDSARS.
Idan ana iya tunawa a cikin watan Oktobar shekarar 2020 ne matasa a Najeriya suka gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen sashen rundunar yan sanda na ENDSARS da ake zargi da azabtar da matasa a sunan yaki da muggan laifuka kamar su damfarar yanar gizo, lamarin da ya rikide ruwa tarzoma har ya kai ga rasa rayuka.