Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin 'Yan Sa Kai Na Kashe Gobara Na Da Muhimmanci A Kasuwanni-Olola


Controller General of Federal Fire Service (FFS), Jaji O Abdulganiyu
Controller General of Federal Fire Service (FFS), Jaji O Abdulganiyu

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Jaji Olola Abdulganiyu, ya kai ziyarar gane wa ido da jajantawa kan gobarar da ta cinye manyan kasuwanni biyu a Maiduguri, inda ya shawarci ‘yan kasuwan da su kafa kungiyar ‘yan kwana-kwana ta sa kai don dakile matsalar.

Ya kuma alakanta yawaitar asarar dukiyoyi da rashin hanyoyin da za su bai wa jami’an agajin gaggawa damar shiga kasuwar domin kashe gobarar.

A cikin wata guda an samu tashin gobara daban-daban guda uku a manyan kasuwanni da kuma shaguna hada da sansanonin ‘yan gudun hijira guda biyu wanda suka auku a jihar Borno. Sai dai wadda ta fi girma itace wacce ta auku a kasuwar Litinin da aka fi sani da Monday Market inda aka yi asarar sama da shaguna dubu 12 da wutar ta kurmus.

Borno Burnt Market 3
Borno Burnt Market 3

Abdulganiyu ya ce idan da masu aikin sa kai sun samu horo yadda ya kamata tare da samar musu da kayan aikin kashe gobara, za su iya dakile tsanani da gobarar ta yi tun kafin isowar jami’an kashe gobara.

“Hanya daya tilo da za a iya hana gobara ita ce tabbatar da cewa an samar da mafi saukin na’urori. Tukunyar kashe gobara (Fire Extinguisher) a kowane dayan wadannan shagunan na iya taimakawa sosai don rage aukuwar gobara.

Bornon Burnt Market 2
Bornon Burnt Market 2

"Kananan horo kan yadda ake amfani da kayan aiki yana da mahimmanci a koyaushe saboda yawancin wuta kan fara ne da kadan, ba babba ba, kuma idan ba ku san abin da za ku yi ba, ta na karuwa," in ji shi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa nan ba da dadewa ba jami’ansa za su fara horas da ‘yan kasuwar aikin sa kai kan yadda ake amfani da barguna da na’urorin kashe gobara.

Wasu ‘yan kasuwa da gobarar ta lakume dukiyoyinsu sun yi kira ga gwamnati da ta tallafa musu da wurin farfado da kasuwancinsu musamman a cikin wannan wata na azumi kana wasu suka ce gwamnati ta gaggauta gyaran kasuwar.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00

XS
SM
MD
LG