Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Hallaka Mutane 26 A Jihar Borno A Harinta Na Farko A Bana


Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane 26 da suka hada da dan sanda daya da masunta a wasu hare-haren ba zato ba tsammani a garuruwan jihar Borno.

A garin Mongumeri, ‘yan ta’addan masu yawan gaske sun kai hari kan tawagar ‘yan sanda ta musamman a ranar Laraba a wani artabu na tsawon sa’a guda, kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta shaida wa Muryar Amurka.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Borno, CP Abdu Umar ya tabbatar da faruwar harin. Ya shaida wa manema labarai cewa an kashe dan sanda a musayar wuta da ‘yan ta’addan. Ya kuma ce, motar ‘yan sandan da ‘yan ta’addan suka yi awon gaba da ita a yayin harin, an samu nasarar kwato motar da taimakon sojojin da ke yankin.

Dakarun Sojojin Najeriya Sun Fatattaki 'Yan Boko Haram Daga Chikun Gudu A Arewacin Borno
Dakarun Sojojin Najeriya Sun Fatattaki 'Yan Boko Haram Daga Chikun Gudu A Arewacin Borno

“Boko Haram sun je Mongumeri suka kai hari a inda muke, wato tawagar mu ta ‘CRACK Team’. Sun zo da yawa, suna harbin bindigogi. Mun yi musayar wuta da su. Mun rasa daya daga cikin mutanenmu amma mun dakile harin. Sun tafi da daya daga cikin motocinmu amma daga baya sojoji sun kwato ta,” inji CP Umar.

Ya ce an dauke gawar dan sandan da aka kashe daga inda aka kai harin.

Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Dikwa a ranar Laraba yayin da Boko Haram suka yi wa wasu masunta kwanton bauna tare da kashe 25 daga cikinsu.

"Daya ya samu rauni kuma yana samun jinya," in ji CP Umar.

Harin Boko Haram
Harin Boko Haram

Wasu mazauna yankin sun ce wadanda harin ya rutsa da su suna diban tarkace da karafa ne a kauyukan da aka lalatar da hare-haren ta’addanci na tsawon shekaru, a lokacin da ‘yan Boko Haram suka yi musu kwanton bauna.

Abubuwan da suka faru sune manyan hare-hare na farko a Borno a bana. Yankin ya sami kwanciyar hankali na dan lokaci.

Ga dai sautin rahoton Haruna Dauda Biu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG